Menene Android Development Darasi na Daya

Android app development image

 Menene Android Development?

 Android development wata hanyace da'ake kirkirar applications wato "Manhajoji" na na'urori dake amfani da operating system na android.

 Ya Ake Hada Android Application?

Kafin kufara haɗa application na android akwai wasu ilimi da ake da bukatar kusani wanda sai mutum ya sansu zai iya hada duk irin application da yake sha'awa.

waƴannan abubuwa sune:

  • Ilimin programming kotlin ko Java
  • Jetpack compose ko Views
  • Ilimin yadda ake amfani da Android Studio
  • Ilimin Firebase  domin sanin yadda za'a adana bayanai na application a yanar gizo gizo
  • Ilimin Google Play Console domin sanin yadda zaka tura app naka a play store
Ta ina yakamata kufara koyan Android Application?

Akwai ɓangarori biyu da ake hada android application wanda kamfanin google ya sahale ake amfani dasu acikin manhajar su ta haɗa application wato "Android Studio".

 waƴannan hayoyi  sune ta amfani da programing language na "Java" ko "kotlin" da kuma yadda ake gina tsaring design na application da "Jetpack compose" ko "View xml"

Idan zaka hada android app da kotlin to wajen tsara design na app zaka iya amfani da view xml ko jetpack compose, idan kuma da java kakeso zakayi amfani da view xml.

Wanne akafi amfani dashi yanzu wajen hada Application?

Kowanne ana amfani dashi wajen haɗa app amma google sun zabi kotlin da jetpack compose wajen tsara da gina application sabo da kayan aiki na jetpack compose da kotlin programming nada  saukin amfani, saurin haɗa app, da ƙayatarwa wajen design.
Sabo da haka muma acikin wannan shafi namu zaku koyi yadda ake hada applicaton na android da kotlin da jetpack compose.

Wane kayan aiki kuke buƙata domin fara koya?

Na'urar computer  kaɗai ake da buƙadar kanema sai kuma data dazaka hau yanar gizo gizo domin sauke Android Studio.

Na'urar computer din kuma anaso takasance :

  • processor nata asamu intel core i3, i5, i7 mai speed kamar 2.4ghz 
  • RAM kamar 8GB
  • Hard disk so samu SSD


Comments